Yadda kofato ke kasuwa a Niger

Ana dafa kofato a tukunya
Image caption Don ya yi laushi idan za a dafa kofaton a kan zuba masa kanwa

Mai yiwuwa a wadansu sassa na duniya idan aka yanka dabba, kofato (ko tako) na cikin abubuwan da ake zubarwa, amma lamarin ya sha bamban a wani sashe na Nijar.

A unguwar Bagalam da ke birnin Maradi na Jamhuriyar ta Niger, babbar sana'ar mutanen daya daga cikin gidajen da ke unguwar—a bangaren 'Yan Rinji (mahauta), ita ce sayar da danyen kofaton dabbobi.

Daya daga cikin matan gidan ta shaida wa wakiliyar BBC, Tchima Illa Issoufou, cewa su kan sayi mudun (ko tiyar) kofato a kan dala 100 na kudin CFA (kwatankwacin dalar Amurka daya da centi 10) su kuma su sayar akan dala 120 CFA.

Yayin da wadansu ke sayar da danye, wadansu kuwa dafawa suke yi kafin su sayar.

Daya daga cikin masu wannan sana'a, Malama 'Yar Kura, ta bayyana cewa jikawa ake yi a sanya kanwa a dafa—shi kuma dala 1,250 na CFA (kwatankwacin dalar Amurka uku) ake sayarwa ko wacce roba.

Image caption Buhu-buhu, ko mudu-mudu, ake sayar da busasshen kofato a unguwar Bagalam

A cewar Malama 'Yar Kura, "kawai kwadayi ne" ya sa ake cin kofaton, "ba yunwa ba".

"Dadi!" Abin da wata da ke cin gyararren kofaton ta shaida wa wakiliyarmu tana ji ke nan. Ta kyalkyace da dariya sannan ta kara da cewa, "Kin san dai gidan [mahauta] ba a yunwar nama. Yadda kika san farin kwai—bayan kwai in an bambare shi, haka nake jin shi".

Don jin cikakken rahoton, sai ku je Sashen Shirye-shiryenmu ku latsa Shirin Safe.