Dan Nigeria na neman mafaka a Birtaniya

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Image caption Sai dai hukumomin Burtaniyar ba za su taso keyar Isa Mu'azu ba sai an tabbatar da yana da lafiyar da zai iya tafiya ta jirgin sama.

Lauyoyi a Burtaniya na fafutika ta bayan fage ta ganin sun ceto ran wani dan Najeriya da ke neman mafaka a kasar bayan yunkurin da suka yi a baya bayan nan ya taimaka aka yi masa sassaucin karin wa'adin kwanaki biyu a Burtaniya.

Shi dai dan Najeriyar mai suna Isa Mu'azu ya shafe kwanaki 90 ne cur yana yajin cin abinci inda yanzu nauyinsa yake a kan kilogram 50, lamarin da ya sa baya ko gani ko iya tsayuwa da kafafunsa.

An dai shirya tasa keyarsa zuwa Najeriya ne a wani jirgin sama na Virgin Atlantic da yammacin Laraba, sai dai yanzu an jinkirta har sai zuwa gobe juma'a.

Shi dai Mu'azu yayi zargin cewa matukar aka dawo da shi Najeriya zai iya fuskantar hari daga 'ya'yan kungiyar Boko Haram wadanda ya ce sun hallaka 'yan uwansa da dama.

Karin bayani