Ana shirin lalata makaman gubar Syria a teku

Wasu daga cikin makaman gubar Syria
Image caption Lalata makaman dai aiki ne da zai ci makudan kudi wadanda gwamnatin Syria ta ce ya kamata Amurka ta samar.

An tsara wani shiri kan yadda za a lalata wani bangare na tarin makaman gubar Syria a cikin teku.

Majiyoyi sun shaida wa BBC cewar a shirin za a kafa wata cibiyar lalata makamai ta tafi-da-gidanka a cikin wani jirgin ruwan yakin Amurka inda za a garwaya sinadaran da ruwa har sai gubarsu ta wanke ta yadda za a iya watsar da su a fili.

Hukumar Haramta Kera Makaman Guba a duniya ta saka wa'adin daga nan zuwa karshen shekara don ta kawar da sidaran guba daga Syria.

Amma ya zuwa yanzu kasashen na jan-kafa wajen karbar aikin lalata su kuma ba a san yadda za a iya fitowa da makaman gubar daga cikin Syria ba ana tsakiyar yakin Basasa.

Karin bayani