Shinawatra ta tsallake rijiya da baya

Firaiministar Thailand Yingluck Shinawatra
Image caption Masu zanga-zangar dai na zargin tsohon Firaiministan kasar wanda dan uwan Shinawatra ne cewa shi ke mulki ta bayan fage.

Firaiministar kasar Thailand Yingluck Shinawatra ta tsallake rijiya da baya a wata kuri'ar yanke-kauna da aka yi a majalisar dokokin kasar da safiyar Alhamis din nan, yayin da aka shiga rana ta biyar ta zanga-zangar nuna adawa da gwamnatinta.

Ta samu nasarar samun kuri'un da take nema a majalisar cikin sauki daga wakilan jam'iyyarta ta PT da kuma abokan kawancenta.

A makon jiya ne jam'iyyar adawa ta DP ta gabatar da bukatar jefa kuriar domin amincewa ko yanke kauna kan iyawar gwamnatinta, a yayin da zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta kankama a manyan titunan babban birnin kasar Bangkok.

Masu zanga-zangar wadanda suka mamaye wasu ma'aikatun gwamnati, sun ce za su dan huta da ga gangamin da suke a yau.

Karin bayani