Kabila ya soma rangadi a Congo

Image caption Shugaba Joseph Kabila

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Joseph Kabila yana rangadin yankin da a baya ya kasance karkashin ikon 'yan tawayen M23 wadanda sojojin gwamnati suka ci da yaki a watan da ya gabata.

Ana sa ran zai isa yankin Rutshuru dake kusa da iyaka da Uganda wurin da a da yan tawayen suke da karfi.

Wannan ziyarar itace ta farko da Mr Kabila zai gabashin kasar cikin shekaru biyu.

Ya shafe makon da ya gabata a cikin ayarin motoci 70 daga Kisangani zuwa yankunan da a da 'yan tawaye keda karfi.

Karin bayani