EU ta gargadi Rasha a kan Ukraine

Image caption Jose Manuel Barosso

Shugabannin Tarayyar Turai-EU sun yi gargadin cewa ba zasu amince da katsalandar din kasar Rasha ba a tattaunawarsu ta karfafa dangantaka da Ukraine.

A karshen taron kolin da tarayyar Turan ta gudanar a Lithuania, shugaban hukumar tarayyar Turan, Jose Manuel Barroso, ya ce ba za a lamunci wani ya shiga tsakanin tattaunawa tsakanin tarayyar Turan da wata kasa ba.

Barroso ya ce "Abinda ba zamu amince da shi ba, shi ne sharadi a kan yarjejeniyar kasa da kasa ta kasance wata kasa ta dabam ta zamanto mai wani abu makamancin hawa kujerar na ki kanta."

Shi dai shugaban kasar Ukraine, Viktor Yanukovych ya ce matsin lambar kasar Rasha ce ta sa a makon jiya ya ki rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hada gwiwa da tarayyar Turai.

Karin bayani