Kungiyar Abzinawa za ta kawo karshen tsaigata wuta a Mali

Wata kungiyar 'yan tawaye ta Abzinawa a kasar Mali ta ce za ta kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta da ta kulla da gwamnati a cikin watan Yuni.

Kungiyar ta yi shelar ne kwana daya bayan an raunata mutane da dama a wata arangama da aka yi tsakanin sojojin kasar ta Mali da Abzinawa dake bore.

Abzinawa sun hana fira ministan kasar kai ziyara garin Kidal na arewacin kasar babban yankin dake hannun 'yan tawayen.

'Yan tawayen sun bayyana tashin hankalin da aka yi a matsayin wata sheilar yaki.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta biyo bayan tsoma bakin da sojojin Faransa suka yi, suka fatattaki mayakan 'yan aware da 'yan kishin Islama a arewacin kasar ta Mali.