'Ana samun ci gaba wajen yaki da AIDS'

Image caption Kwayar cutar HIV mai rikedewa ta zama AIDS

Wani sabon rahoto da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya fitar ya nuna cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kare jariran da ke cikin mahaifansu daga kamuwa da cutar kanjamau.

Rahoton ya ce a shekarar 2005 zuwa 2012 yara dubu 850 ne suka kaucewa kamuwa da cutar HIV a kasashe marasa karfi da matsakaita.

Haka kuma rahoton na bana mai taken 'Alaka tsakanin kananan yara da cutar HIV' ya nuna cewa a yanzu yara matasa ne suke cikin hadarin kamuwa da cutar Kanjamau.

Rahoton na UNICEF ya yi kira ga kasashe da su kara kaimi wajen rage yaduwar cuta HIV da kuma AIDS a tsakanin al'umma.

Karin bayani