'Dole ne Boko Haram su dakatar da kai hari'

Kungiyar Boko Haram
Image caption 'Kungiyar Boko Haram na amfani da kananan yara domin yaki'

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta ce tayi hira da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa kimanin mutum 60.

Mutanen sun hada da ma'aikatan lafiya da kungiyoyin kare hakkin dan adam na cikin gida da komandojin rundunar hadin gwiwa da kuma ma'aikatan gwamnati a lokacin da ta kai ziyara biranen Kano da Maiduguri kafin ta tattara bayanan ta

Kuma komandojin sojin sun fada mata cewa sun kubatar da mata 26 da suka hada da 'yan mata daga maiduguri da kuma gandun dajin Sambisa.

Rahotan na 'Human Rights Watch' ya ce shaidu sun fada musu cewa sun ga kananan yara a lokutan da 'ya'yan kungiyar suke kai hare hare.

A birnin Maiduguri 'Human Right Watch' tace wani abu mai daure kai shine wani bidiyo da ta gani, na wani yaro dan shekaru 14 da jami'an tsaro suke masa tambayoyi wanda yake bayanin irin rawar da yake takawa a yakin da 'ya'yan kungiyar suke yi.

Rahotan yace komandojin sojin sun bayyana cewa sun kubutar da yara irinsu da dama a lokacin da suka kai hari a dajin nan na sambisa.

Dangane da haka ne 'Human Right Watch' tace tace dole ne 'yan Kungiyar su dakatar da kai hare harenu ba tare da wani bata lokaci ba, sannan su saki dukkanin kananan yara da matan dake hannusu.

Dole ne Gwamnati ta yi bincike

Rahotan na 'Human Right Watch' ya yi kira ga gwamnatin Najeriya data gudanar da cikakken bincike wanda babu son rai a cikinsa, game da zargin ganawa mutane azaba harma da mu tuwarsu a lokacin da suke tsare.

'Human Right Watch' tace tace alhakin gwamnatin Najeriya ne karkashin dokokin kare hakkin dan adam na Kasashen duniya, don haka dole ne ta dauki matakan da suka dcae na kare 'yan kasa daga duk wani tashin hankali, amma ba ta hanyar amfani da karfin daya wuce kima ba, ko kuma azabtarwa.

Rahotan yace dole ne kuma gwamnatin Najeriya ta gurfanar da duk wadanda suka aikata laifuka a lokacin tashe tashen hankulan da suka hada da jami'an tsaro da kuma kungiyoyin 'yan banga, wadanda gwamnati ke marawa baya.

Haka kuma dole ne hadin gwiwar rundunar tsaron sa kai na farin kaya wato 'civilian joint task force' ta dakatar da daukar kananan yara wajen murkushe aikace aikacen tadakayar baya.