Adawa da dokar haramta zanga zanga a Masar

Zanga zangar adawa a birnin Alkahira
Image caption Zanga zangar adawa a birnin Alkahira

Yan sandan Masar sun harba hayaki mai sa hawaye akan wasu masu fafukar kare hakkin bil Adama wadanda ke zanga zangar nuna adawa da sabuwar dokar da ta haramta zanga zangar a birnin Alkahira.

'Masu fafutukar sun yiwa zanga zangar take da cewa "A shirye muke mu mika kanmu"

Suna maida martani ne ga wata doka da babban mai gabatar da kara ya gabatar ga masu zanga zangar a farkon wannan makon.

Sabuwar dokar ta bukaci masu zanga zanga su nemi izini daga 'yan sanda tukunna kwanaki uku kafin gudanar da dukkan wani taron gangamin da ya kai adadin mutane goma ko fiye da haka.

Karin bayani