'Yan sanda a Ukraine sun tarwatsa masu zanga-zanga

Ukraine
Image caption Masu zanga-zanga a Ukraine

'Yan Sanda a kasar Ukraine sun tarwatsa wasu masu yi wa Shugaba Victor Yuna-Kovich bore a Kiev babban birnin kasar.

An raunata mutane da dama lokacinda 'yan sanda suka yi amfani da kwagiri don tarwatsa taron kimanin mutane dari hudu dake zanga-zanga da sanyin safiya.

Tun farko, wasu dubban mutane sun hallara a dandalin 'yancin kai don nuna rashin amincewarsu ga kiyawar da Shugaban kasar ya yi, ya amince da wata yarjejeniyar hadin-gwiwa da Tarayyar Turai.

Mr Yunakovich ya ce matsin lamba ce daga Rasha ta sanya shi daukar matsayin.

'yan adawa sun ce ya hana kasar cimma mafarkin ta na matsawa kurkusa da tarayyar Turai.