Allah ya yi wa Nelson Mandela rasuwa

Image caption Mandela shi ne bakar fata na farko da ya shugabanci Afrika ta Kudu

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela ya rasu. Gwamnatin Afrika ta Kudu ce ta bayar da sanarwar mutuwar a daren ranar Alhamis.

Nelson Mandela wanda a shekara ta 1994, ya zama shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko, ya dade yana fama da laulayi, ga kuma yawan shekaru.

An daure shi ne bisa laifin hada baki domin hambarar da gwamnatin farar fata 'yan tsiraru ta mulkin wariyar launin fata.

Shugaba Mandela dai yana da tarihi na rashin lafiyar huhu, tun daga lokacin da ya kamu da cutar tarin fuka a gidan kurkuku.

Karin bayani