An kashe masu kishin Islama a Mali

Mayakan masu kishin Islama a Mali

Rahotanni daga Mali sun ce sojojin Faransa sun kashe masu tsatstauran ra'ayin addinin Muslunci 19 a yankin arewacin kasar.

An ce sojojin na Faransa sun kaddamar da wani hari ne a kan dakarun masu tsattsauran ra'ayin a arewa da birinin Timbuktu.

A farkon bana ne dai sojojin Faransa suka jagoranci wani yunkuri da ya fatattaki dakarun masu tsattsauran ra'ayin da na 'yan aware daga birane da garuruwan arewacin kasar ta Mali.

Sai dai kuma masu tsattsauran ra'yin wadanda ke dauke da makamai na ci gaba da kai hari a kan sojojin Faransa, da na kasashen Afirka, da na kasar ta Mali.