Erdogan ya soki biniken cin hanci a Turkiya

Pirayim Minista Tayyip Erdogan na Turkiya
Image caption Pirayim Minista Tayyip Erdogan na Turkiya

Pirayim Ministan Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya soki matakin gudanar da bincike game da zargin mummunan cin hancin da ke faruwa a cikin gwamnatinsa,yana mai bayyana matakin da cewa bai dace ba.

Mr Erdogan Ya shaidawa wani taron manema labarai cewa ba zai lamunci duk wani zagon kasa na siyasa ba, ya kuma ce wasu mutane na son yin zagon kasa ga tagomashin da Turkiya ke samu na jerawa da manyan kasashen duniya a ci gaban tattalin arziki.

Shi ma mataimakin Mr Erdogan ya jaddada fushin gwamnati game da binciken, wanda yace akwai siyasa a ciki,ya kuma kara da cewa.

An dai kama mutane da dama a wani samame a ranar Talata,da kuma dakatar da manyan jami'an 'yansada biyar a matsayin maida martani, da Mr Erdogan ya ce an yi musu hakan ne saboda sun sabawa ka'i'ojin aiki.