A yau ake bikin yaki da cutar AIDS ko CIDA

world aids day
Bayanan hoto,

Bikin yaki da cutar AIDS ko CIDA na bana

Hukumomin kiwon lafiya da masu ba da agaji a fadin duniya suna bukin shekara-shekara na ranar yaki da cutar dake karya garkuwar jiki watau AIDS KO CIDA ta duniya,

Manufar ranar ita ce a gudanar da bukukuwa da wasu abubuwa da nufin kara fadakar da mutane game da cutar.

A cikin wata sanarwa, babban Daraktan hukumar yaki da cutar CIDA ta Majalisar Dinkin Duniya Michel Sidibe ya ce sannu a hankali ana shawo kan cutar da ta mamaye duniya.

To amma ya yi gargadin cewa har yanzu ana nuna kyama da tauye wa masu dauke da cutar hakkokinsu.

Mutane fiye da miliyan arba'in a duk fadin duniya ke dauke da kwayoyin cutar.