An harba hayaki me sa hawaye a kan masu zanga-zanga a Thailand

Thailand
Image caption Masu zanga-zanga a Thailand

Gwamnatin kasar Thailand ta tura dubban sojoji su tallafa 'yan sandan kwantar da tarzoma wajen kare ma'aikatu a Bangkok babban birnin kasar.

An harba hayaki me sa hawaye don hana masu zanga-zanga mamaye gidan gwamnati.

Masu zanga-zangar dai sun shiga gidajen talabijin da dama kuma wasu rahotanni sun ce suna kokarin sasantawa yadda za su karbe aikin watsa shire-shire.

Wani wakilin BBC a Bangkok ya ce wannan yunkurin ya yi kama da harkokin da ake yi a juyin mulki.

An kashe akalla mutume biyu a arangamar da aka yi jiya tsakanin magoya baya da masu kiyayya da gwamnatin.