'Yan Boko Haram sun kashe mutane 20 a Borno

Nigerian soldiers
Image caption Abubakar Shekau na Boko Haram

Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar nan ne da aka fi sani da Boko Haram sun kashe mutane sama da ashirin a jihar Borno .

Rahotanni na cewa maharan sun kashe mutane 7 a kauyen Doron Baga da ke gabar tafkin Chadi.

Sun kuma ce an kona tarin kwalele da ragar kama kifi da mazauna garin ke amfani da su wajen aiwatar da sana'arsu ta kamun kifi.

Kamfanin dillanci labarai na AFP ya ce maharan sun yi kwanton bauna ne, inda suka kashe mutane kuma su ka jikkata wasu da dama.

Haka kuma a kauyen Sabon Gari da ke karamar hukumar Damboa maharan sun kashe mutane goma sha 17 ranar alhamis din da ta gabata.

Sai dai saboda rashin layukan sadarwa a jihar ta Borno ba a samu labarin ba a kan lokaci.

Kusan mutane dari biyu aka kashe a watan Afrilun da ya gabata a lokacin da aka yi artabu tsakanin 'yan boko haram da sojojin a garin Baga.

Kashe-kashen na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin kasar ta lashi takobin tsaurara matakan tsaro saboda matsowar bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.