Kundin tsarin mulkin Masar

Masar
Image caption Mambobin kwamitin da aka dorawa alhakin rubuta daftarin kudurin tsarin mulki na Masar

An amince da wani daftarin kudurin tsarin mulki a kasar Masar, za a kuma kaada kuri'ar raba gardama kansa a badi.

A yayinda kwamitin da aka dora wa alhakin rubuta tsarin mulkin ke muhawara a kan sauye-sauyen karshe ga tsarin mulkin, an yi ta zanga-zanga a dandalin Tahrir.

A dandalin Tahrir ne 'yan sanda suka harba hayaki me sa hawaye don tarwatsa magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Mursi.

Sabon tsarin mulkin, ya cigaba da aiki da jerin iko da dama da aka ba sojojin kasar wadanda suka hada da tuhumar farar hula a wasu lokutan.

Zai zamo wajibi dai a gudanar da sabon zabe cikin watanni shidda bayan amincewa da sabon tsarin mulkin kasar.