Najeriya: Ba mu hana jirgi sauka ba

Ministar sufuri ta Najeriya Stella Oduah
Image caption Ministar sufuri ta Najeriya Stella Oduah

Hukumomin sufurin jiragen saman Najeriya sun musanta rahotannin kafofin yada labaran Birtaniya cewa sun hana jirigin nan dake dauke da dan Najeriya Isa Mu'azu dake neman mafaka a Birtaniya sauka a Najeriya.

Hukumomin Birtaniya sun tasa keyar Isa Mu'azu zuwa gida ne duk da yajin cin abinci da yake yi, yana cewa, yana tsoron idan ya koma Najeriya 'yan kungiyar Boko Haram zasu iya kashe shi, amma wannan dalili bai gamsar da hukumomin Birtaniya har su ba shi mafaka ba.

Mista Yaukubu Dati kakakin hukumomin sufurin jiragen saman Najeriya, kuma yace, Najeriya ba ta hana jirgin sauka ba.

Yace abin da ya faru shine hukumomi basu kammala shirye-shiryen da suka kamata ba a saboda haka ne matukin jirgin ya sauka a Malta domin jira a kammala shir-shiryen.

Yace gwamnatin Najeriya ta bada dukkanin dama kuma da zarar jami'an Birtaniya sun kammala shirye shirye jirgin zai kamo hanya zuwa Najeriya

Karin bayani