Masu keken NAPEP sun ce ba a yi adalci ba

Jami'an tsaron nijeriya
Image caption Jami'an tsaron Nijeriya

Kungiyar masu sana'a da Keken NAPEP a Abuja Najeriya ta maida martani a kan sakamakon bincike da kwamitin da majalisar dattawan najeriya ta kafa dangane kashe-kashen da ake zargin jami'an tsaro sun yi wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba a Unguwar Apo dake Abuja.

Tun farko dai 'ya'yan Kungiyar ne suka yi zargin cewa jami'an tsaron sun karkashe masu mutane da sunan 'yan Kungiyar Boko Haram a wani samame da suka kai wurinda suke kwana.

To sai dai sakamakon binciken na 'yan majalisar ya wanke jami'an tsaron da aikata wani abinda ya saaba ma doka kuma ya ce jami'an tsaron sun kare kansu ne.

Alhaji Buba Usman Goza, shugaban Kungiyar masu sana'ar ta Keken NAPEP a Abuja, yace babu adalci ko kadan a cikin rahoton, saboda babu wata shaida da ta tabbatar da ikirarin da jami'an tsaron suka yi.

Karin bayani