Takaddama kan kundin tsarin mulki a Masar

Image caption 'Yan kungiyar Muslim Brotherhood

Kungiyar 'yan Uwa Musumai a Masar ta yi watsi da sabo kundin tsarin mulki kasar da aka rubuta, wanda ranar talata za'a gabatarwa shugaban kasar na rikon kwarya, Adly Mansur.

Kungiyar 'yan uwa Musulmai ta ce kundin tsarin mulkin kasar na baya da aka amince da shi a karkashin gwamnatinsu shi ne halattace.

Sabon kundin tsarin mulin da za'a yi zaban jin ra'ayin jama a akansa wata gobe ya kara wa sojoji karfi.

Tilasne ministan tsaro ya kasance soja ne, haka kuma za'a yi yiwa fararan hular da suka kai wa sojoji hari a kotunan soji.

Haka nan kuma a sabon kundin tsarin mulkin za'a yi amfani da shari'ar musulunci a wajan yin dokoki.

Karin bayani