'Za a baiwa jirgin da zai sake dauko Mu'azu iznin sauka'

Isa Mu'azu
Image caption Mu'azu ya yi ta kokarin hana tisa keyarsa zuwa Najeriya

Mahukuntan Najeriya sun ce idan gwamnatin Burtaniya ta sake maida dan Najeriyar nan Isa Mu'az dake neman mafaka a kasar za'a ba jirgin ya kai shi izinin sauka.

Ranar juma'ar da ta gabata ma'aikatar cikin gidan Burtaniya ta yi hayar wani karamin jirgi mai zaman sama domin a mayar da Isa Muazu Najeriya, amma aka hana jirgin sauka sabilida jami'ai sun ce ba'a kammala cike takaddun zuwan jirgin Najeriya ba.

Isa Mu'azu ya yi ta kokarin hana tisa keyarsa zuwa Najeriya, inda ya shiga yajin cin abinci sama da wata uku.

Jami'ai a Najeriya sun ce ba su san ko za'a sake kai Isa Mu'azu Najeria ba.