An kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Maiduguri

'Yan Boko Haram
Image caption kawo yanzu wasu na ganin dokar ta-baci ta kasa magance matsalar tsaro a yankunan da gwamnati ta tura dubban sojoji.

Gwamnatin jihar Borno da ke arewacin Najeriya ta kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a birnin Maiduguri da kewaye, tun daga ranar Litinin bayan da 'yan Boko Haram suka kaddamar da hare-hare da asuba.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Ahmed Jidda, ya fitar, ta ce an kafa dokar hana fitar ce bayan gwamnati ta tuntubi jami'an tsaro a kan lamarin.

A cewar sanarwar, "dokar hana fitar ta zama wajibi ne saboda hare-haren da 'yan Boko Haram suka kaddamar a safiyar yau."

Sanarwar ta bukaci al'ummar jihar su kwantar da hankali a yayin da gwamnati ke kokarin shawo kan matsalar.

A watan Mayu ne, Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a Borno da wasu jihohi biyu a kokarin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Sai dai kawo yanzu, masu sharhi na ganin cewar dokar ta kasa magance matsalar tsaro a yankunan da gwamnati ta tura dubban sojoji.

Karin bayani