An kashe mahara 24 a Maiduguri

Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan sansanin sojin saman kasar da ke birnin.

Hedikwatar tsaron kasar ta tabbatar da mutuwar mahara ashirin da hudu yayin da sojoji biyu suka jikkata.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Borno ta ba da sanarwar kafa dokar hana fita ta sa'o'i ashirin da hudu a fadin brnin na Maiduguri.

Mazauna birnin na Maiduguri sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa a cikin birnin tun da misalin karfe daya na daren ranar Lahadi.

An kuma ba da rahoton cewa daruruwan 'yan bindiga wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da harin da misalin karfe daya na dare a kan sansanin sojin sama na Najeriya da ke birnin.

'Ya shafi farar hula'

Image caption Shekau ya amsa cewar sune suka kai wasu hare-hare a baya

A cewar rahotanni harin ya ritsa da mutane da dama ciki har da wasu daga cikin maharan da aka halaka a cikin motocin da suka yi amfani da su wajen kai harin.

Bincike dai ya tabbatar da cewa harin ya fi muni a wurare biyu da suka hada da sansanin sojin saman Najeriya da ke makwabtaka da filin saukar jiragen saman kasar da kuma Barikin sojojin kasa mai 3-3 barrack da ke wajen birnin na Maiduguri.

Wasu da suka ga abin da ya faru sun ce an kona kusan baki dayan gine-ginen da ke barikin, kuma ana fargabar cewa harin ya ritsa da mutane da dama.

Kokarin ji ta bakin Hedikwatar tsaron Najeriya kai tsaye ya ci tura, amma wasu bayanan da hedikwatar ta yi cikin wata sanarwar da ta fitar sun ce an jikkata jami'an soji biyu a lokacin harin, yayin da aka kashe mahara ashirin da hudu.

Kazalika rundunar ta ce an lalata wasu jiragen yaki uku da rundunar ta daina amfani da su da kuma wasu jirage masu saukar ungulu biyu.

'Dokar hana fita'

Ita ma gwamnatin Jihar ta Borno a nata bangaren ta ba da sanarwar kafa dokar hana fita ta sa'o'i ashirin da hudu a kwaryar birnin na Maiduguri, lamarin da ya tilasta wa matafiya da dama da ke kan hanyarsu ta zuwa birnin na Maiduguri karya linzami sakamakon dokar da aka kafa.

A bangaren guda kuma, hukumar da ke kula da filayen saukan jiragen saman Najeriya ta tabbatar da cewa harin bai shafi filin saukan jiragen saman kasar da ke birnin na Maiduguri ba, amma duk da haka ta rufe filin zuwa wani lokaci saboda dalilai na tsaro.

Image caption Jihar Borno na karkashin dokar ta-baci

Shi ma shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya gana da hafsoshin tsaron kasar sakamakon wannan harin.

Babu dai wani bayani a kan abin da suka cimma, amma hafsoshin tsaron sun tabbatar da cewa an shawo kan lamarin.

Wannan hari na zuwa kwanaki kadan bayan da rundunar sojin Najeriya ta ce ta kai hare-hare a dajin Sambisa, inda suka ce 'yan kungiyar ta Boko Haram na da sansani.