'Assad na da hannu a aikata laifukan yaki'

Bashar al Asad
Image caption Ofishin Ms Pillay na rike da wani jerin sunayen wadanda ake zargin masu aikata laifukan yaki ne

Kwamishinar kula da hakkin dan Adam a Majalisar dinkin duniya Navi Pillay a karon farko ta ce Shugaba Bashar al-Asad na Syria nada hannu a zargin aikata laifukan yaki da kuma laifuka akan bil-adama a Syria.

Ta ce binciken da hukumarta ta gudanar a watanni sha takwas din da suka gabata, ya gano hujjar dake nuna cewa yana da alhaki a matakin kololuwa

Kwamishinar ta ce dukkanin bangarorin dake cikin rikicin sun keta hakkin bil adama, amma lamarin ya fi girma ta bangaren gwamnati.

Ofishin Ms Pillay na rike da wani jerin sunayen wadanda ake zargin masu aikata laifukan yaki ne, amma ba za a saki sunayen ba har sai an kaisu gaban Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya

Karin bayani