Arafat ya rasu ne sakamakon ajali amma ba guba

Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat
Image caption Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat

Wasu alkalai da kotunan Faransa suka nada domin gudanar da bincike a kan mutuwar tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat a shekara ta 2004, sun yi watsi da hasashen da ake yi cewa an kashe shi ta hanyar ba shi guba.

Hukuncin alkalan dai ya saba wa sakamakon binciken da wasu kwararru suka gudanar a Switzerland a watan jiya, wanda ya ce mai yiwuwa gubar Polonium ce ta kashe Mr Arafat.

Wakilin BBC a Paris ya ce Babban jami'in nan da Hukumar mulkin Falasdinawa ta nada domin gudanar da bincike a kan mutuwar Mr Afarat din, ya ce ya kusa kammala nasa binciken, kuma nan da 'yan kwanaki masu zuwa zai bayyana sunayen mutanen da ya yi imanin cewa suna da hannu a mutuwar Mr Arafat.

Karin bayani