'Yan Boko Haram sun yi wa sojoji barna

Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

'Yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kadammar da hare-hare a garin Maiduguri na jihar Borno a sansanin sojin sama, inda suka lalata helikoftoci biyu da kuma jiragen soji uku.

Sanarwar da kakakin rundunar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Chris Olukolade ya fitar, ta ce 'yan Boko Haram din sun kai harin ne a cikin dare har zuwa wayewar garin ranar Litinin, amma kuma jami'an tsaro sun yi kokarin dakile harin.

A cewarsa, sakamakon batakashin, an kashe 'yan Boko Haram 24 a yayin da sojoji biyu suka samu raunuka.

Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewar, an yi gumurzu sosai, kuma bisa dukkan alamu an samu asarar rayuka da dama a lokacin artabun.

Mazauna birnin na Maiduguri sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa a cikin birnin tun da misalin karfe daya na daren ranar Lahadi.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Borno ta ba da sanarwar kafa dokar hana fita dare da rana a fadin birnin na Maiduguri.

Karin bayani