An sassauta dokar hana fita a Maiduguri

Image caption Jihar Borno na karkashin dokar ta baci

Gwamnatin jihar Borno dake arewacin Nigeria ta sassauta dokar hana fita da ta kafa a Maiduguri, babban birnin jihar, kwana guda bayan da 'yan Boko Haram suka yi barna a sansanin sojin saman kasar dake birnin.

Sakataren gwamnatin jihar, Baba Ahmed Jidda, wanda ya bada sanarwar ya ce a yanzu dokar hana fitar za ta soma aiki ne daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe.

A ranar litinin aka kafa dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 a Maiduguri, bayan da 'yan Boko Haram suka kadammar da hare-hare a kan jami'an tsaron inda suka lalata helikoptoci biyu da jiragen saman sojin uku.

Ko da yake dai jami'an tsaro sun ce sun kashe maharan 24 amma kuma wasu rahotanni sun nuna cewar, an yi mummunar barna sakamakon artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan Boko Haram.

Haka kuma an maido da layukan salula a birnin a ranar Talata.

Karin bayani