An zargi hukumar CIA da azabtarda fursunoni a Poland

Image caption 'An gana ma fursunonin azaba matuka a gidan kurkukun'.

A karon farko jamaar dake halartar zaman wata kotu sun saurari zarge-zargen da aka yi cewa Hukumar leken asirin Amurka, CIA ta yi amfani da wani gidan kurkuku na sirri a kasar Poland domin azabtar da fursunoni.

Kotun kare Hakkin Bil adama ta Turai dake birnin Strasbourg ta saurari zarge-zargen cewa gwamnatin Poland ta kyale jami'an Hukumar ta CIA suna yiwa wadanda take zargi da ta'addanci tambayoyi a gidan kurkukun dake cikin wani daji mai nisa a Arewacin kasar ta Poland a shekara ta 2002.

Lawyoyin wasu fursunoni 2 da aka tsare a sansanin Guantanamo, sun ce an gana ma fursunonin azaba matuka a gidan kurkukun.

Karin bayani