Ilimi: Daliban Asia ne gaba a duniya

Image caption Finland ita ce kadai a nahiyar Turai da ta shiga cikin kasashe biyar da ke gaba

Kasashen nahiyar Asiya sune kan gaba a darussan lissafi da kimiyya da nazarin littattafai kamar yadda wani binciken ilmi na duniya ya nuna.

Rahotan (na OECD) wanda ya yi nazari akan yara rabin miliyan masu shekaru goma sha biyar a kasashe sittin da biyar ya nuna cewa dalibai daga Shanghai birni mafi girma a China sune na farko, sai kuma na Singapore da Hongkong da Taiwan da Koriya ta Kudu da ke biye masu.

Kasar Finland ita ce kadai a nahiyar Turai da ta shiga cikin kasashe biyar da ke gaba a darasin Kimiyya kawai.

Burtaniya wacce take kashe kudade fiye da kima akan harkar ilimi ta samu maki matsakaici.

Rahotan na ya ce kasashen da suka fi samun nasara akan harkar ilmi sune wadanda suke gagarumin kokarin wajen daga matsayin yara marassa galihu.