Korea ta Arewa ta kori wani kusa a gwamnati

 Kim Jong-un da Jang Song Thaek
Image caption Ana ganin Jang Song Thaek shi ne kashin bayan ikon gwamnatin Kim Jong-un

Rahotanni daga Korea ta Kudu na cewa an cire daya daga cikin manyan 'yan siyasar Korea ta Arewa wanda kuma kawun shugaban kasar ne kim Jong-un daga ofis.

An kori Jang Song-Thaek daga mukamin mataimakin shugaban hukumar tsaro, daya daga cikin muhimman hukumomin kasar.

Wani daga cikin 'yan majalisar Korea ta Kudu ne ya bayyana wannan labari bayan bayanai da hukumar leken asiri ta korea ta kudun ta tsegunta musu.

Sau da dama ana ganin hoton Jang Song-Thaek a kusa da shugaban kasar ta Korea ta Kudu .

Kawo yanzu dai babu wasu bayanai game da dalilan korar shi.

Wasu rahotanni sun ce daman an kashe wasu makusantan Mr Jang kuma shi ma tun lokacin ba a ganinsa a bainar jama'a.

Idan dai wannan labari ya tabbata, hakan na nufin wani gagarumin sauyi a gwanatin Korea ta arewan da ke gudanar da harkokinta cikin sirri.

Koma dai ya labarin ya kasance hukumar leken asiri ta Korea ta Kudu a baya ta bayar da labaran da ke kasancewa ba haka ba.

Siyasar Pyonyang dai aba ce da ke wakana cikin sirri kuma akan dauki lokaci kafin gaskiyar al'amura ta bayyana.