Syria ta karyata majalisar dinkin duniya

Image caption Syria ta ce an shirya zargin ne don asa matsin lambar siyasa a kan gwamnati

Mataimakin Ministan harkokin waje na Syria, Faisal Mekdad, yayi watsi da zargin Majalisar dinkin duniya cewar Shugaba Bashar Al-Assad ne da kansa keda alhakin laifukan yaki a Syria.

Ya shedawa BBC cewar gwamnati ba za ta damu da kare hakkin Bil Adama a lokacin da take tinkarar yan-ta'adda daga wasu wuraren duniya tare da samun tallafi daga Kasashen Saudiya da Qatar ba.

Ya ce zargin na kwamishinar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar dinkin duniya, Navi Pillay an shirya shi ne don sa matsin lambar siyasa a kan gwamnati gabanin tattaunawar zaman lafiyar Majalisar dinkin duniya da aka shirya yi a Geneva a cikin mako mai zuwa.

Mutane da dama ne dai suka hallaka a yakin da ake yi a Syria yayinda dubun dubatar mutane ke gudun hijira ala tilas a wasu Kasashen dake makwabtaka da Syrian.

Karin bayani