Rashawa: Afghanistan da Somalia ne kan gaba

Image caption Alkaluman suna nuna cewar lamarin ya fi muni a Afrika

Kasashen Afghanistan da Koriya ta Arewa da kuma Somalia su ne ake kallo a matsayin kasashen da suka fi kowanne cin hanci da rashawa a duniya.

Alkaluman da kungiyar yaki da rashawa ta kasa da kasa, Transparency International ta fitar, sun nuna cewar kasashen Denmark da New Zealand sune suka fi gaskiya wajen tafiyar da dukiyar al'umma.

Nigeria ce kasa ta 144 cikin 177 da ake cin hanci da rashawa a yayinda Niger kuma ta 106 sai Ghana a matakin na 63.

A cikin kasashe 177 da kungiyar ta gudanar da bincike a kansu, kusan kashi 70 cikin 100 na da babbar matsalar cin hanci da rashawa.

Kasashen da lamarin yafi mune sun hada da Iraki, Syria, Libya, Sudan, Sudan ta Kudu, Chadi, Equatorial Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Turkmenistan, Uzbekistan da kuma Yemen.

Sannan kuma kasashen da suka ciri tuta wajen kwatanta gaskiya su ne; Denmark, New Zealand, Luxembourg, Canada, Australia, Netherlands, Switzerland, Singapore, Norway, Sweden da kuma Finland.

Karin bayani