Rikici a Afrika ta Tsakiya na dada ruruwa

Image caption Jamhuriyyar Afrika ta TSakiya na dada rikicewa

Rikicin da ake yi a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya kara ruruwa, inda ake zargin mayaka 'yan kungiyar Seleka da kai hare-hare kan mabiya addinin kirista a wani kauye da suka hallaka akalla mutane biyar.

A karshen makon da ya gabata kuma wani harin na daban ya hallaka mutane goma sha biyu.

Wakilin BBC da ke babban birnin kasar Bangui, ya ce daruruwan mazauna kauyuka ne suka gudu daga muhallinsu, inda suke boye a cikin dazuzzuka inda suke rokar kasashen waje su kai musu dauki.

Wasu 'yan kwarya-kwaryar dakarun wanzar da zaman lafiya na Afrika su na jiran a kara yawansu, duk da Faransa ta tura karin dakarunta.

A nan gaba ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan batun.

Karin bayani