CDS ba za ta yi taron Congres ba

Alhaji Mahamane Ousmane, CDS Rahama
Image caption Alhaji Mahamane Ousmane, CDS Rahama

A Nijar jam'iyyar CDS Rahama ta ce ba za ta kira babban taronta na Congres ba, sai bayan kotu ta warware rikicin shugabancin da ke tsakanin bangaren shugaban jam'iyyar Alhaji Mahamane Ousmane da na mataimakinsa Alhaji Abdou Labo.

Ministan cikin gidan Nijar din, wanda kuma shi ne ke kula da jam'iyyun siyasa, ya bukaci CDS din da ta shirya taron nan da ranar Juma'a don kada ta keta doka.

Kotu dai ta soke Congres na karshe da jam'iyyar ta yi a shekara ta 2011 a Damagaram saboda a cewarta ba a yi shi kan ka'ida ba.

Shugaban jam'iyar Alhaji Mahamane Ousmane ya ce bai amince da shi ba, ya kuma daukaka kara a gaban kotun ECOWAS.