Dubban 'Yan Eritrea aka sace a hamadar Sinai'

Image caption Jakadan Eritrea a Birtaniya,Tesfamichael Gerahtu, ya amsa kasancewar matsalar

Wani sabon rahoto ya nuna cewar 'Yan Eritrea kusan dubu talatin ne aka sace sannan kuma aka gana masu akuba a hamadar Sinai a cikin shekaru hudun da suka wuce.

Dola akalla miliyan 600 ne aka tatsa daga hannun iyalansu a matsayin kudin fansa.

Wata tawagar malaman jami'o'i da kuma masu fafutikar kare hakkin bil adama daga Sweden da Holland sun gabatar da sakamakon bincikensu ga majalisar dokokin Turai.

Sun gano cewar an tilasta wa da yawan wadanda aka yi garkuwar da su su buga wa danginsu waya yayinda ake azabtar da su .

Jakadan Eritrea a Birtaniya,Tesfamichael Gerahtu, ya amsa kasancewar matsalar, amma ya shedawa BBC cewar wata makarkashiya ce ta dagangan da wadanda ke wajen kasar ta Etritrea ke amfani da ita domin kawo rarrabuwa a kasar.