EU za ta dauki matakan kare 'yan ci rani

'Yan cirani
Image caption 'Yan cirani na mutuwa a cikin teku a kokarin shiga Kasashen Turai

Tarayyar Turai ta bada sanarwar tsaurara sintirin iyakokinta na teku da kuma kara yin hobbasa domin kara taimakawa masu neman mafaka.

Wadannan canje canjen na zuwa ne watanni biyu bayan da daruruwan 'yan cirani suka mutu a lokacin da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a gabar tsibirin Lampedusa na Kasar Italiya.

Shawara ita ce ta samar da wata dabara ta bai daya ta inganta sa-ido daga Cyprus zuwa Spain domin gano jiagen ruwan da suke cikin mawuyacin hali da sauri

Kwamishinar harkokin cikin gida Cecilia Malmstorm ta bayyana matakan da cewa wani martanin Turai ne na gaskiya da ka iya samar da wani canji.

Dole ne Shugabannin Tarayyar Turai su bada amincewarsu ga shirin a wani Taro da za a yi a Brussels a wannan watan.

Karin bayani