Zaben jiha ya dauki hankali a India

Image caption Zabe a India na jan hankali

Masu zabe a babban birnin India Delhi, za su kada kuri'ar zaben dan majalisar Jiha wanda zaben ana ganin wani gwaji ne ga zaben kasar na shekara mai zuwa.

Hankula sun karkata akan Jam'iyyar da ke rajin yaki da cin hanci wato Common Man Party wadda ta tsayar da dan takara a karon farko.

Mara baya ga Jam'iyyar na sama da kasa a ra'ayoyin jama'a amma wasu na ganin Jam'iyyar za ta iya zama mai karfi.

Jam'iyya mai mulki ta Congress Party na neman mukamin karo na hudu a jere a zaben na birnin, ita kuwa Jam'iyyar adawa ta BJP zaben zai zama wani gwaji ne ga sabon jajirceccen shugaba (Narendra Modi)

Karin bayani