An gargadi Isra'ila kan rusa gidaje

Matsgunan Israila
Image caption Palasdinawa fiye da 300 sun rasa matsugunansu

Kungiyar masu rajin kare hakkin bil-adama su 36 sun bukaci Isra'ila da ta dakatar da rusa gidajen Palasdinawa gabanin ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.

Sun ce tun daga lokacin da aka dawo da tattaunawar zaman lafiya a watan Yuli, Isra'ela ta rusa gidaje fiye da dari biyu a gabar yamma da kogin jordan da aka mamaye.

Sannan Palasdinawa fiye da 300, wadanda fiye da rabinsu mata ne da kananan yara sun rasa matsugunansu.

Masu rajin kare hakkkin bil-adam sun ce akan yi rusau din ne domin bada hanyar fadada matsugunan

Karin bayani