Boko Haram: Za a yi wa mutane 500 shari'a

An dai kakkama mutanen ne lokacin farmakin da sojojin suka kai wa jihohin Yobe da Borno da Kuma Adamawa
Bayanan hoto,

An dai kakkama mutanen ne lokacin farmakin da sojojin suka kai wa jihohin Yobe da Borno da Kuma Adamawa

Hukumomin soji a Najeriya sun bayar da sunayen wasu mutane dari biyar da ake zargi da 'yan kungiyar Boko Haram ne domin yi musu shari'a.

A cikin wata sanarwa da ya aike wa kafafen watsa labaran kasar Daraktan sashen watsa labarai na ma'aikatar tsaron Najeriya Birgediya Janar Chris Olukolade ya ce mutanen su 500 na daga cikin wasu

kamammu 1400 da wata tawagar hadin gwiwa ta jami'an tsaron kasar ta tantance a wuraren tsare mutane daban-daban tsakanin watannin Yuli da Satumba na wannan shekarar.

Da ma dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi sukar yadda hukumomin kasar ke ci gaba da tsare wadanda suke tuhuma da zama 'yan kungiyar ta Boko Haram ba tare da kai su gaban kotu ba.