Daurin shekaru 7 kan masu suka a Facebook

Image caption Miliyoyin 'yan Nigeria na amfani da shafin Twitter

Majalisar dattawan Nigeria na kokarin daukar wasu tsaurara matakai da nufin hana aikata miyagun laifuka ta hanyoyin sadarwa na yanar-Gizo ko internet.

Kudirin dokar da majalisar ke kokarin zartarwa na neman a hukunta wanda aka samu da laifin damfara ko ingiza al'umma ta yi wa gwamnatin kasar tawaye ta yanar-Gizo daurin shekara bakwai ko kuma a yi masa tarar naira miliyon biyar.

'Yan Nigeria da dama ne suke amfani da shafukan zumunta na zamani a intanet kamar facebook da twitter kuma gwamnati na kallon wasu daga cikin masu amfani da shafukan a matsayin barazana.

Dino Melaye wani mai fafutuka a shafin Twitter ya ce "Gwamnati na neman rufe bakin wasu mutane amma ta rasa yadda za ta yi, shi yasa take son kafa wannan dokar".

Harwa yau kudirin dokar ya yi tanadin daurin shekara bakwai ga duk wanda aka kama da laifin damfarar jama'a ta hanyar amfani da internet.

Majalisar ta yi kudirin dokar karatu na biyu da kuma zaman sauraron ra'ayin jama'a, matakin da zai bai wa kwamitin hadin-gwiwa na musamman da majalisar ta kafa damar daidaita ire-iren ra'ayoyin da ya tattara don gabatar wa majalisar kafin a san makomar kudirin.

Karin bayani