Amurka: Ba za mu yaki Boko Haram ba

Image caption 'Ba za a tsananta bincike kan 'yan Najeriya dake tafiye tafiye zuwa Amurka ba'

Gwamnatin Amurka ta ce bata da niyyar amfani da jirage marasa matuka ko kuma sojojin kasar ta wajen yakar 'yan kungiyar Boko Haram.

Kwamandan rundunar sojin Amurka dake aikin wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afrika wato AFRICOM Janar David M. Rodriguez ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da wasu jami'an ma'aikatar tsaron Amurka ke yi a Najeriya.

Ya ce 'abin da muke da niyyar yi shi ne mu taimaki 'yan Najeriya su kaifafa kwarewarsu ta yadda za su dakushe kalubalen Boko Haram'.

Hakazalika jami'an Amurkan sun ce basa ganin ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda zai sa a kara tsananta ko wanne irin bincike a kan 'yan Najeriyar da ke tafiye-tafiye zuwa Amurka.

Tun bayan da gwamnatin Amurka ta ayyana kungiyar Jama'atu Ahlussuna Liddawati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ne dai jama'a da dama ke nuna damuwa na cewa mai yiwuwa Amurka ta yi amfani da jiragen yakin ta marasa matuka ko kuma sojojin ta wajen yakar 'yan kungiyar.

Su dai jami'an gwamnatin Amurkar na ziyara a Najeriyar ne don tattaunawa da hukumomin tsaron kasar kan hanyoyin da Amurkar zata tallafa musu a gwagwarmayar da suke yi da masu tada kayar baya.