Ana zaman dar-dar a Bangui

'yan tawayen kungiyar seleka
Image caption Ana fargabar barkewar rikicin musulmi da kiristoci a kasar

An yi harbe harbe da kuma amfani da manyan makamai a babban birnin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Bangui, sa'oi kadan kafin tsammanin da ake na Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura dakarun Afirka da na Faransa kasar.

Wani wakilin BBC a birnin ya ce ya ga manyan motoci dauke da sojoji suna sintiri a titinan birnin kuma galibin mutane na zaune a gidajensu.

Jakadan faransa a Majalisar Dinkin Duniya, Gerard Araud ya sheda wa BBC cewa matakin tura karin dakarun zaman lafiyar zai kawo sauyi a yanayin tsaron kasar cikin makwanni.

Mr Araud ya ce dakarun kasashen Afrikan da na Majalisar Dinkin Duniya za su maido da doka da tsaro a Bangui.