CAR: Za a yi amfani da karfin soji

Motar yaki
Image caption Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar dai ta tsunduma cikin rikici ne a watan Maris

Kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya bai wa sojojin Faransa da na Afirka izinin amfani da karfi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin kare fararen hula.

Kwamitin ya kuma sanya takunkumin hana shigar da makamai cikin Kasar.

Kuma sun nemi majalisar dinkin duniya da ta shirya yiwuwar kai wata rundunar kiyaye zaman lafiya Kasar.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar dai ta tsunduma cikin rikici ne a watan Maris a lokacin da 'yan tawaye suka hambarar da Shugaba Francois Bozize.

An hallaka mutane da dama yayin da fada ya barke tun da farko a yau a babban birnin Kasar Bangui, tsakanin tsoffin 'yan tawaye da kuma magoya bayan Mr Bozize.

Karin bayani