Mandela ya bautawa kasarsa

Image caption Mandela na yi gwagwarmaya a Afrika ta kudu

Nelson Mandela ya fara rayuwarsa ne a yankin kauyen Transkei dake Afrika ta kudu.

Ya sami horo ne a matsayin lauya a Jami'a daya tilo wadda ake barin dalibai bakaken fata suyi karatu.

Daga bisani ya shiga Kungiyar African National Congress wadda a lokacin kungiyar siyasa ce wadda take sukar gwamnatin wariyar launin fata.

An yi wa Nelson Mandela daurin rai da rai kan aiyukan da ya yi na yaki da wariyar launin fata ya kuma shafe shekaru ashirin da bakwai a gidan yari.

An sallame shi a 1990 sannan ya zama zababben shugaban kasar Afrika ta kudu na farko bayan shekaru hudu.

Ya kuma sauka bayan da ya yi wa'adi daya na shekaru biyar amma ya ci gaba da kasancewa mutum mai fada a ji kuma wanda ake girmamawa.

Karin bayani