Ivory Coast ta nemi jirage marasa matuka

Image caption Akwai yiwuwar kara jirage marasa matuka inda ake rikice-rikice

Jagoran tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ta yiwu a kara yawan jirage marasa matuka na tattara bayanai a wuraren da suke gudanar da ayyukansu kuma ake fuskantar tashe-tashen hankula a wurin.

Herve Ladsous ya shaidawa BBC cewa yanzu haka kasar Ivory Coast ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kai jirage marasa matuka kasar.

Ya kuma ce akwai hanyoyi da dama da za a iya amfani da jiragen.

Ladsous, yace "ina ganin a bayyane take cewa zamu san abinda ke faruwa ta dalilin wadannan jirage tare da bunkasar ayyukanmu musamman ma Sojoji, sannan wadanda suke lura da wannan aiki don su san abinda ke faruwa."

Karin bayani