Mutane 15,000 sun rasa matsugunansu a Diffa

Image caption Ambaliyar ruwa da aka yi a Yamai a shekara ta 2012

Mutane kusan 15,000 ne suka rasa matsugunansu a jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar sakamakon ambaliyar ruwa daga rafin Komadugu.

Cikin kwanaki 20 da rafin na Komadugu ya cika ya batse, ya na ta ambaliya lamarin da ya shafi iyalai fiye da 2,000.

Rahotanni sun nuna cewar ambaliyar ta lalata makarantu da gonaki da kuma tituna.

Sakamakon wannan ambaliyar dai farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi.