Red Cross na neman agajin kudi

Red Cross
Image caption Wasu kudaden da Red Cross ke nema za su tafi ne zuwa Somalia

Hukumar ba da agaji ta Red Cross ta duniya na neman taimakon kudaden da suka haura dala biliyan daya domin tallafa wa ayyukan ta na jinkai a yankunan da yaki ya daidaita a shekara mai zuwa.

Kaso mafi yawa na kudaden zai tafi ne zuwa Syria.

Shugaban hukumar Red Cross din ya bayyana rikicin da ake fama da shi a Syria da cewa ya yi munin gaske.

Kasashen Afghanistan da Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Somalia na cikin Kasashe na gaba-gaba da za su ci moriyar kudaden.

Har ila yau Hukumar Red Cross din ta ce za ta mai da hankali kwarai wajen tallafa wa wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar yin lalata da su da kuma wadanda aka jikkata da wadanda suka rasa matsugunansu da kuma wadanda aka tsare.

Karin bayani