Sarkin Thailand ya ja kunnen 'yan kasar

Image caption An ja hankailin 'yan Thailand kan ci gaban kasa

Shahararren Sarkin Thailand, Bhumibol Adulyadej ya bukaci al'ummar kasar da su tallafi juna don cigaban kasarsu.

Ana bikin cikar Sarkin shekaru tamanin da shida a duniya, bayan kwashe kwanaki ana gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Bangkok.

Da yake jawabi a Fadarsa da ke wajen Shakatawa na gabar teku da ke Hua Hin Mr Adoon-yadet yace al'umar Thailand na zaune da juna lafiya saboda hadin kan da ke tsakaninsu.

Masu zanga-zangar dai na kokarin hambarar da gwamnatin Yingluck Shinawatra, inda suke zarginta da kasancewa mai bin maganar dan uwanta Thaksin Shinawatra tsohon Prime Ministan kasar wanda ya yi gudun hijira.

Karin bayani