Shugabannin kasashen duniya sun nuna alhini

Image caption Mandela tare da tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton

Tuni dai shugabannin kasashen da hukumomi na duniya suke ta bayyana alhininsu dangane da rasuwar tsohon shugaban kasar na Afirka ta Kudu, Nelson Mandela.

Shugaba Obama na Amurka ya bayyana cewa duniya ta yi asarar daya daga cikin gwarazan da ke da karfin fada-a-ji, da jarunta.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon kuwa cewa ya yi yana matukar jimamin rasuwar Nelson Mandela, wanda ya kwatanta da wani jarumi da ya tsaya tsayin daka don tabbatar da adalci.

Firaministan Birtaniya, David Cameron ya bayyana Mandela a matsayin daya daga cikin fitattun mutane a duniya wanda haduwa dashi babban martaba ce.

Shi ma Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya cewa ya yi rasuwar Mista Mandela gagarumar asara ce ga nahiyar Afirka.